Labarai

An kama jiga-jigan jam’iyyar APC na fatan ina ma Buhari ya mutu

An kama jiga-jigan jam’iyyar APC na fatan ina ma Buhari ya mutu

Daga Manuniya

Shugaban riko na jam’iyyar APC reshen karamar hukumar Yola ta Kudu, Sulaiman Adamu, yayi fatan ina ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya mutu. A cewarsa inda son samu ne yaso a ce cutar korona ta kashe shugaban kasar.

Majiyar MANUNIYA Daily Nigerian ta wallafa cewa an jiyo jiga-jigan APC suna ta caccakar shugaba Buhari ne a wani taro da sukayi shekaran jiya.

A cikin sautin murya da aka nada ba tare da sanun su ba, an jiyo Adamu, yana fadin cewa Osinbajo ya fi Buhari amfani, kuma da za a basu zabi tsakanin Osinbajo da Buhari to da Osinbajo zasu dauka.

Manuniya ta tattaro daga DN shima wani jigo a APC Abubakar Sirimbai ya soki shugaban kasar har ma yana fadin cewa dama Buhari ya mutu Osinbajo ya karbi kasarnan domin babu abunda Buhari ya tsinana wa jihar Adamawa tun hawansa mulki shekara 6.


Surumbai ya kara da cewa Sun yi da nasanin yin bakin kokarinsu don ganin yaci zabe kodayake dama ance bakin mugu ne domin an ce Buhari har murna yake yi idan yaji wani ya talauce.

Shima tsohon kakakin majalisar jihar Adamawa Mijinyawa an jiyo shi a cikin sautin muryar yana fadin cewa dama kam Osinbajo nasu ne.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button