Labarai

An dakatar da Shugaban APCn da aka kama yana fatan ina ma Buhari ya mutu

An dakatar da Shugagab APC da aka kama yana fatan ina ma Buhari ya mutu

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito Jam’iyyar APC ta dakatar da shugaban Jam’iyyar APC reshen jihar Yola ta Kudu Suleiman Adamu bisa kamasashi yana yiwa caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari har ma yana yi masa fatan ina ma ya mutu

Manuniya ta ruwaito dakatarwar ta fito ne daga kakakin jam’iyya na jihar Adamawa, Mohammed Abdullahi, bayan wani zaman gaggawa da jiga-jigan jam’iyyar sukayi a yau Talata Jim kadan da bayyanar sautin muryar shugaban jam’iyyar yana sukar Buhari wanda tuni ya karade kafafen sadarwa.

Ya ce an nada Adamu Majekano a matsayin sabon shugaban jam’iyyar har zuwa lokacinda za a kammala binciken lamarin

A dazu ne dai Manuniya ta ruwaito maku yadda aka nadi muryar Adamu yana sukar shugaban kasar har ma yana fatan ina ma korona ta kashe shi Osinbajo ya karbi kasar domin babu abunda jihar Adamawa ta amafana da mulkin Buhari tsawon shekara 6

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button