Album/EPHausa SongsLabarai

Wata mata a Jigawa ta cinna wa kanta wuta ‘saboda mijinta zai ƙara aure’

Wata mata a Jigawa ta cinna wa kanta wuta ‘saboda mijinta zai ƙara aure’

Rahotanni daga jihar Jigawa na bayyana cewa wata mata mai suna Maimuna Wadaji ta cinna wa kanta wuta da zummar kashe kanta da kanta saboda mijinta zai ƙara aure.

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Lawan Shiisu, ya faɗa wa manema labarai cewa matar ta aikata laifin ne a ranar Juma’a da ta gabata a ƙauyen Runguma na garin Dutse, babban birnin jihar Jigawa.

Sai dai tuni aka garzaya da ita asibiti kuma tana cen kwance a halin yanzu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button