Labarai

An dage ranar komawa makaranta a Kaduna har sai yadda hali yayi

An dage ranar komawa makaranta a Kaduna har sai yadda hali yayi

Daga Manuniya

Gwamnatin jihar Kaduna ta baiwa dalibai da iyaye hakuri cewa ba za a bude makarantu a ranar 9 ga watan Augusta ba kamar yadda aka tsara tun farko.

A wata sanarwa da dauke da sa hannun kwamishinan ilimi na Kaduna,  Shehu Usman Muhammad ya fitar ya ce za a fadi sabuwar ranar da za a koma makarantu a fadin jihar.

Manuniya ta ruwaito haka zalika za a dakatar da ayyukan da ake gudanarwa a wasu wurare dake fama da matsalar tsaro.

Gwamnatin ta dauki wannan mataki ne saboda shawarar da ma’aikatar tsaro ta bayar cewa sojoji na sintiri a iyakokin Kaduna/Niger/Katsina/Plateau da Zamfara domin kakkabe yan bindiga da barayin daji dake addabar yankin.

“Gwamnatin jihar Kaduna tana godiya ga ma’aikatar tsaro kana tana kira ga jama’ar jihar Kaduna da su cigaba da bayar da hadin kai domin kaiwa gaci”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button