Labarai

Evans yace wa kotu shi dan kasuwa ne ba kidinafas ba

Evans ya shaidawa kotu cewa shi attajirin dan kasuwa ne ba kidinafa ba

Daga Manuniya

Kasurgumin Biloniyan mai garkuwa da mutane da aka kama a Lagos a 2017, Chukwudimeme wanda aka fi sani da ‘Evans’ Onwuamadike ya karyata zargin da ake yi masa na garkuwa da mutane inda ya shaidawa Kotu a yau Talata cewa shi ba kidinafa bane, shi dan kasuwa ne mai saye da sayar da kayan ado da kyale-kyale. Don haka bai ma san tuhumar garkuwa da mutane da ake yi akansa ba, sharri ne ake masa.


Evans da tawagar Lauyoyinsa a karkashin Victor Okpara, ya ce sharri Gwamnatin jihar Lagos ke yi masa amma a zahirin gaskiya shi dan kasuwa ne.

Manuniya ta ruwaito ya cigaba da cewa shi sunansa ba Evans ba kuma bashi da wani suna na daban bashi da wani take ko lakani kwata-kwata sannan kuma shi mazaunin, Fred Shoboyede Street ne dake Magodo Phase II, a jihar Lagos mai sana’ar sayar da kayan ado da kyale-kyale

A cewarsa yan sanda ne suka tsorata shi ta hanyar kashe wasu mutum 4 a gaban idanunsa sannan suka sa shi ya amsa cewa shi mai garkuwa da mutane ne a 2017 da suka kama shi. Ya kuma ce bai san mutane biyar da aka hadashi dasu ba cewa wai abokan sana’arsa ne, ya ce bai ma taba ganinsu ba kawai an gabatar dasu ne cewa wai yaransa ne da suke taya shi yin kidnafin.

Alkalin Kotun ya dage shari’ar zuwa ranar 5 ga watan Nuwamba domin cigaba da sauraron karar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button