Labarai

Alhakin Kanawa ne ya kama Abba Kyari –inji Kwankwaso

Alhakin Kanawa ne ya kama DCP Abba Kyari –inji Kwankwaso

Daga Manuniya

A yayin da kowa ke bayyana ra’ayinsa game da zargin dambarwar dake faruwa da babban dan sanda DCP Abba Kyari, Tsohon Gwamnan Kano jagoran Kwankwasiyya Rabiu Musa Kwankwaso shima yabi sahu inda yace alhakin yan Kwankwasiyya ce ta kama dan sandan.

Kodayake dai bai ambaci suna ba amma dai anga bidiyon Tsohon Sanata Kwankwaso na cewa duk wadanda suka taimaka wajen murde masu zabe a 2019 a Kano ta hanyar inconclusive yanzu suna girbar abunda suka shuka don jiya ma yaji an dakatar da daya daga aikinsa [Abba Kyari kenan).

Shafin Kwankwasiyya na Kwankwasiyya Reporters ya wallafa wani rubutu da ya jaddada rahoton Manuniya inda shafinsu na Facebook ya rubuta cewa “Operation Girbi abinda ka shuka”

“Operation din zai maida hankaline gurin zakulo irin gudunmawar da wasu su ka bayar a zaben inconclusive na Kano da kuma irin yadda su ke girbe abubuwan da su ka shuka. Sai dai operation din zai dagawa wadanda su ka mutu kafa. Da fari dai mu fara da wannan:

1. Ministan da ya baiwa IG umarnin ayi rashin arzikin, ya bar kujrrar.

2. IG din da aka baiwa umarnin, ya bar kujerar.

3. DIG (dan giya) din da aka aiko shima ya bar kujerar.

4. Abba Kyari da su ka taimakawa DIG shima an dakatar da shi.

5. Singham da aka hana yin aikin sa sabo da shi mai gaskiya ne, ya yi ritaya cikin aminchi kuma yanzu ya na rike da kujerar mai baiwa gwamnan Gombe shawara akan harkokin tsaro. 

A saurari sako na gaba.

Daga Kabir Dakata” kamar yadda Manuniya ta ruwaito shafin ya rubuta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button