in

IGP ya nemi a dakatar da DCP Abba kyari daga aiki

IGP ya rubuta takardar dakatar da DCP Abba kyari daga aiki

Daga Manuniya

Shugaban yan sandan Nigeria, IGP Usman Baba, ya nemi a dakatar da DCP Abba Kyari bisa zargin cin hanci da rashawa da ake yi masa domin samun damar a binciken shi.

Sufeta-Janar din ya aikewa hukumar kula da harkokin yan sanda yana neman su amince da dakatarwar. Sannan ya kafa kwamitin mutum 4 da zasu gudanar da binciken.

Sanarwar ta ce har yanzu a wajen ta DCP Abba bashi da laifi har sai an kammala bincike kan zargin harkalla da kasurgumin mai damfara, Ramon Abbas Hushpuppy.

DA DUMI-DUMI: Kungiyar Izala ta umurci limaman Juma’a suyi addu’oi na musamman kan Sahara Reporters da Afenifere

DA DUMI-DUMI: An dakatar da DCP Abba kyari daga aiki