Labarai

DA DUMI-DUMI: An dakatar da DCP Abba kyari daga aiki

Rundunar yan sanda ta dakatar da DCP Abba kyari daga aiki

Hukumar kula da sha’anin yan sanda ta Nigeria PSC ta dakatar da DCP Abba Kyari daga aiki har zuwa lokacinda za a kammala bincike bisa zarginsa da FBI ke yi na karbar cin hanci

Kakakin hukumar PSC, Ikechukwu Ani, ne ya sanar da haka a Lahadi a Abuja, ya ce dakatarwar tana kunshe a wata takarda da Sufeta-Janar na yan sandan Nigeria ya aike wa hukumar mai lamba PSC/POL/D/153/vol/V/138

Kuma kwamishina na daya na hukumar PSC, Justice Clara Ogunbiyi, ya sanya wa hannu nan take a madadin shugaban hukumar Musiliu Smith.

Manuniya ta ruwaito PSC ta nemi IG ya rika bata bayanin halin da ake ciki na binciken da rundunar yan sandan ke yiwa DCP Abba domin sanin mataki na gaba da zata dauka akansa. Matakin dai ka iya kaiwa ga kora daga aiki muddin aka same shi da laifi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button