Labarai

Wata Kotu a Amurka ta umurci FBI ta cafko mata DCP Abba Kyari

Wata Kotu a Amurka ta umurci FBI ta cafko mata DCP Abba Kyari

Daga Manuniya

Rahotannin na bayyana cewa wata Kotu a kasar Amurka ta baiwa jam’ian tsaron Amurka FBI umurni su cafko mata babban dan sandan Nigeria da yayi fice wajen yaki da yan ta’adda DCP Abba Kyari bisa zarginsa da karbar cin hanci daga wani kasurgumin dan damfara Hushpuppi.

Kodayake dai DCP Abba ya musanta zargin tare da cewa bai karbi ko sisi a wajen Hushpuppi ba amma jaridar Desertherald ta ambaci Peoples Gazzette ta ruwaito cewa Alkali Otis Wright ya bada umurni a cafko mata shi a kawo gabanta.

Ramon Olorunwa Abbas wanda aka fi sani da ‘Ray Hushpuppi’ ya shaidawa kotun California cewa ya bawa DCP Abba Kyari cin hancin wasu kudade domin ya kama wani abokin huldarsa Vincent.

DCP Abba dai ya hakikance cewa sau daya harkalla ta taba hadashi da Hushpuppi kuma shima lokacinda ya hadashi da wani Tela ne inda shi Hushpuppi ya bayar da dinki kuma ya turawa Telan kudin dinkin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button