Addini da RayuwaLabarai

Takaitattun Labarun Safe

TAKAITATTUN LABARUN SAFE DAGA MANUNIYA

Jama’a Barkanmu da safiyar ranar Alhamis, ga labaran duniya a takaice, domin samun labarai kai tsaye ko tattaunawa kan labarun mu ku biyo mu a shafinmu na Facebook www.fb.com/manuniyanews ko Instagram @manuniyanews


PLATEAU: Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a kafa asibitin kashi da tsoka, Orthopaedic Hospital a Jos babban birnin jihar Plateau.


ABUJA: Dala tayi tashin gwauron zabi bayan da Gwamnan babban bankin Nigeria CBN, Godwin Emefiele, ya sanar da matakinsu na daina sayarwa ƴan canji kuɗaɗen ƙetare saboda hada-hadar kuɗin da ya ce ana yi ta haramtacciyar hanya. A ranar Talata da Laraba dala ta koma naira 522 maimakon 505 da take a da.NASARAWA: Mutum 8 sun mutu, sannan ana ci gaba da laluben fiye da 15 cikin sama da mutum 30 da ruwa ya yi awon gaba da su sakamakon wani mamakon ruwan sama mai tafe da iska da aka fuskanta a garin Keffi na jihar Nassarawa ranar Litinin.SOKOTO: Jami’an tsaro na NSCDC sun samu nasarar kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane wanda ake nemansa ruwa a jallo, Bello Galadima a Sokoto.BORNO: Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya baiwa matasa yan asalin jihar Borno su 641 da suke neman aikin soja daga kananan hukumomi 27 dake jihar tallafin N12.8m, sannan zai rika biyansu dubu 15 a duk wata har su yi passing out.


KADUNA: Yan bindiga sun kashe dan takarar shugabancin karamar hukumar Kachia, Alamkah Dominic Usman a Keffi-Akwanga yana hanyar zuwa Benue. Margayin shine dan takarar APC a zaben kananan hukumomi da za ayi a ranar Asabar 14 ga watan Augusta 2021NASARAWA: Hukumar EFCC ta kama tsohon Gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura, da matarsa Mairo Al-Makura bisa zargin badakala. Al-Makura ya rike Gwamnan Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 inda aka zabeshi Sanata mai wakiltar Nasarawa ta Kudu.


DAGA MANUNIYA

KATSINA: Ana fargaban akalla masu yiwa kasa hidima 5 ne suka mutu a wani hadarin mota da ya rutsa dasu a Katsina lokacinda suke hanyar zuwa sansanin da aka tura su daga jihar Uyo, wadanda suka ji rauni suna kwance a asibitin Kwari General Hospital.


LABARAN KUDANCIN NIGERIA

ONDO: Shugaba Muhammadu Buhari ya taya zababben Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu murna bisa nasarar da ya samu a kotun koli. Sauran wadanda suka taya shi murna sun hada da Abokin karawarsa, Jagade, APC, da jam’iyyar PDP kodayake PDP ta hada da sukar shari’ar amma tace ta dauki kaddara.


IMO: Rundunar yan sandan jihar Imo ta sanar da kama wani sojan IPOB, Obumneke Gabriel. Kakakin yan sanda a jihar Micheal Abattam, yace an kama wanda ake zargin da bindiga da wasu makamai.


ANAMBARA: Akalla mutum 1 ya mutu kana wasu 14 sun ji rauni a wani hadarin mota da ya auku a Upper Iweka dake Onitsha a jihar Anambra.


EDO: An sace wasu sojojin ruwa 7 a jihar Edo lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa jihar Kaduna daga Delta. Kodayake ‘yan sanda daga bisani sun ce sun yi nasarar kubutar da mutum biyar daga cikinsu


LABARAN KASASHEN WAJE

TOKYO: An koro yan wasan tseren Nigeria su 10 daga gasar Olympic dake gudana a Tokyo bisa zargin rashin cancanta

AMURKA: Yan majalisar Amurka na yunkurin hana Gwamnatin kasar sayarwa da Nigeria wasu jiragen yaki kirar 12 AH-1 Cobra da sauran makaman tsaro da kudinsu ya kai dala $875 million, yan majalisar na zargin Gwamnatin Buhari da tauye hakkin dan Adam.


BENIN: Shugaban kasar Benin, Patrice Talon, ya bayyana cewa a shirye yake domin baiwa Nigeria dukkan goyon bayan da take bukata domin yaukaka danganta a tsakanin kasashen biyu. Talon ya fadi haka ne a lokacinda yake karbar jakadan Nigeria a Benin Tukur Buratai.


AMURKA: Babban jami’in Nigeria a kasar Amurka, Lot Egopija, yace sun fara shirye-shirye domin yiwa yan Nigeria mazauna Amurka rejistar NIN, kamar yadda Ministan sadarwa, Isa Pantami ya umurta. A ranar 31 ga watan Octoba ne dai za a rufe yin NIN a Nigeria.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button