Labarai

Sufeta-Janar na yan sandan Nigeria yasa a binci Abba Kyari kan zargin badakala

Sufeta-Janar na yan sandan Nigeria ya fara binciken DCP Abba Kyari kan zargin badakala

Shugaban yan sandan Nigeria IGP Usman Alkali Baba ya bayar da umurni babban sashin rundunar ya binciki DCP Abba Kyari bisa zarge-zargen da ake yi masa na karbar cin hanci a hannun Hushpuppi

Manuniya ta ruwaito kakakin rundunar yan sanda Frank Mba shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar da yammacin yau Alhamis.

Frank ya ce sun samu sammaci daga hukumar tsaron Amurka FBI cewa ana zargin DCP Abba kuma nan take Sufeta-Janar na yan sandan Nigeria ya basu tabbacin zasu bi diddigin batun sannan zasu bayyana sakamakon binciken.

Tuni dai wanda ake zargin DCP Abba Kyari ya musanta karbar cin hancin da Hushpuppi ya ce ya bashi a cikin wasu dala $1.1 miliyan da Hushpuppin ya damfari wani dan kasar Qatar kuma aka kama shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button