KannywoodLabarai

DA DUMI-DUMI: Kungiyar Izala ta umurci limaman Juma’a suyi addu’oi na musamman kan Sahara Reporters da Afenifere

KUNGIYAR JIBWIS TA UMURCI LIMAMAN JUMA’A DA SUYI ADDU’OI NA MUSAMMAN AKAN CIN ZARAFIN DA AFINIFERE DA JARIDAR SAHARA SUKA YIWA ANABI MUHAMMAD (SAW).

Daga Ibrahim Baba Suleiman

Shugaban kungiyar JIBWIS Sheikh Abdullahi Bala Lau ya umurci limaman juma’a da suyi addu’oi na musamman yayin gabatar da huduba akan kungiyar yarbawa ta afinifere da jaridar Sahara na cin zarafin fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW).

Sheikh Bala Lau, ya umarci limaman ne da suyi wadannan addu’oi domin Allah ya wargaza lamarin su, ya kaskantar da su su koma kamar ba’a taba jinsu ba, “kuma muna da tabbacin Allah zai musu hakan insha Allah”Inji shi.

Kazalika Shehin Malami ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dinga daukar matakan gaggawa akan masu takala (Tsokana) wanda hakan shike janyo tashin hankali wanda bama fata. “A karshen karshe muna fatar gwamnati zata saka ido akan muhimmancin zaman lafiyar kasa tare da daukan matakin gaggawa domin dakile rigima.” Inji Sheikh Bala Lau.

A karshe Sheikh Bala Lau ya karkare da kira ga musulmai ‘yan social media da su kauracewa shafin na Sahara Reporters, kowa ya fita a fejin ya kuma mika koke ga hukumar Facebook akan haka, wannan shi zai kawo karshen cin zarafin Annabin Rahama a wannan kasa daga tsageru da yardan Allah.

Allah ya karbi addu’oin da zamu gabatar a juma’ar. Amin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button