KannywoodLabarai

Kungiyar Izala (JIBWIS) ta dauki mataki kan SR da Afenifere bisa batanci ga Annabi

KWATANTA IGBOHO DA ANNABI MUHAMMAD (SAW) ABUN TAKAICI NE DA TADA HANKALI, IZALA TA BUKACI KUNGIYAR AFENIFERE DA SU JANYE KALAMANSU TARE DA BAWA MUSULMAI HAKURI, KAZALIKA TA GARGADI SAHARA REPORTERS KAN WALLAFE WALLAFE MASU TADA RIKICIN KABILANCI KO NA ADDINI A KASA

JIBWIS wacce akafi sani da Kungiyar Izala ta cikaro da wata sanarawa da Kungiyar kare martabar al’adar Yarbawa a Najeriya wato Afenifere tasake wa manema labarai a kwanakinnan. A ta cewar Afenifere, fafutukar da wani mai rajin kafa Kasar Yarbawa a Najeriya, Sunday Igboho yake tafkawa har yasa ya tsallake boda zuwa kasar Benin Republic bayan da hukumar jami’an tsaro na farin kaya DSS suka sanar da nemanshi ruwa a a jallo, yayi kama da irin gwagwarmayar da Annabin Musulunci Muhammad (SAW) yayi na hijira daga garin Makkah zuwa Madinah. Sanarwar, wacce jaridar Sahara Reporters mai yada labarai a yanar gizo ta wallafa, yajawo ce-ce-kuce. A bisa wannan dalili ne na rashin kyautawa daga Afenifere Kungiyar Izala bayan ta fahimci yunkurin cin zarafin Musulunci da kuma tada tarzoma a kasa da kalaman ka iya jawowa babu ghaira babu dalili, taga dacewar fitar da wannan bayanai kamar haka:

  1. Kungiyar Izala tayi fatali da kakkausar harshe da irin wannan rashin ladabi, tsokana da nuna isa daga Kungiyar Afenifere kasancewar babu wani mahaluki a tarihin duniya da ya isa, koma yayi kusa da yaja da kima, daraja da matsayin Annabinmu Muhammad (SAW). Duba da irin wannan munana ladabi ga Annabinmu, da kuma rashin la’akari da mutunta Muslman Najeriya da Kungiyar Afenifere tayi, Kungiyar Izala tuni tayi watsi da lamarin Afenifere tunda sun zabi bada kariya ga dan ta’adda mai yunkurin wargaza Najeriya bayan dukkanin wasu hujjoji dake bayyana alakarsa da ta’addanci sun riga sun bayyana fili. A maimakon Afenifere su barranta kansu da irin wannan Dan ta’,adda, yazama abun mamaki ga kowa yadda suka zabi hanyar ingiza jama’a domin haddasa tarzoma da tashin hankali a kokarinsu na ba dannasu kariya. A dai dai wannan lokaci da Kasar Najeriya take ciki, bai kamaci Kungiyar Afenifere da ire iren wadannan kalamai ba, a don haka, yazama tilas su dawo cikin tai-tayinsu!
  2. Bayan bukatarmu ga Kungiyar Afenifere da ta gaggauta Janye wadannan munanan kalamai, yazama tilas da ta fito ta bada hakuri ga daukacin al-umar Muslumin Najeriya batare da bata lokaci ba.
  3. Kampanin jaridar Sahara Reporters, sun Shahara wajen yayata kazaman wallafe wallafe masu cin zarafi ga addinin Musulunci da Muslumi kuma masu tarnaki ga zaman lafiya da cigaban kasa. Kungiyar Izala tana gargadinsu tare da Jan hankali akan su nesanta kansu daga batanci, munana ladabi, rashin bada damar fahimtar juna da kyautata zamantakewa. A maimakon haka, yazama wajibi su mayar da hankalinsu wajen biyayya ga shimfidaddun tsare tsare da dokokin da suka shafi harkar jarida sannanu a fadin duniya.

Kungiyar Izala ta kara jadadda goyon bayanta ga cigaban Najeriya da zama lafiya. Muddin anaso a samu nasara a kasa, Izala tana tunatar da daukacin al-umar kasar cewa dolene kowa yakoma ga Allaah (SWT) tareda jin tsoronshi da bin umarnin Allah a cikin dabi’u, da mu’amala da ma sauran al-amura na yau da gobe. Kazalika al-umah dolene su zamto masu ilimi da hadin kai kuma masu kyawawan halaye. A ta hakane kadai za’a iya samun cigaba mai dorewa a kasa.

Allah yayimana jagora. Amin.

Sa Hannun: Sheikh, Imam (Dr) Abdullahi Bala Lau
(NATIONAL CHARMAN, JIBWIS NIGERIA)
NHQ, FCT-Abuja.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button