A karshe dai babbar Kotun jihar Kaduna ta wanke tare da sallamar shugaban kungiyar Islamic Movement in Nigeria (IMN), Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat.
Kotun wacce ke Ibrahim Taiwo Road a Kaduna ta umurci a saki jagoran kungiyar shi’ar anan take.