Labarai

MURIC ta buƙaci Afenifere ta janye tare da neman afuwa kan batanci ga Annabi

Muric ta buƙaci Afenifere su nemi afuwa kan ɓatanci ga Annabi, Sahara Reporters ta rasa mabiya dubu 500+

Ƙungiyar kare hakkin Musulmi ta Najeriya, Muric, tayi Allah wadai tare da kira ga ƙungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere ta gaggauta neman afuwa kan kwatanta Annabi da Sunday Igboho, jagora ƴan awaren yarbawa.

Tun a daren ranar Litinin dai ake Allah wadai a kafafen sadarwa biyo bayan fitar da sanarwar Afenifere inda ta kwatanta gudun hijira da Igboho ya yi zuwa Jamhuriyar Benin da wanda Annabi ya yi daga Makkah zuwa Madina.

A wata sanarwa da ta fitar shugaban ƙungiyar, Farfesa Ishaq Akintola, ya ce kalaman Afenifere ɓatanci ne ga addini da Annabi, wanda ba za a lamunta ba.

Jaridar Sahara reporters ce ta soma wallafa wannan ɓatanci da Afenifere ta yi, batun da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kafofin sada zumunta da alla-wadai tsakanin musulmin Najeriya.

Jama’a sunyi wa jaridar caa inda sukayi kira da a kaurace mata kana a daina bibiyar shafin hakazalika an fitar da karar neman shafin Facebook ya goge ta.

Binciken Manuniya ya nuna jaridar daga baya ta saduda inda ta goge labarin da ta wallafar hadi da bayar da hakuri ga musulman Nigeria. Sai dai kawo karfe 10 agogon Nigeria jaridar tayi asarar akalla mabiya dubu 500.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button