Labarai

Izala (JIBWIS) tayi tir da Sahara Reporters da Afenifere

TIR DA WANNAN TAKALA:

Sheikh Dr. Ibrahim Jalo Jalingo

1. Wannan irin takala da gurbatattu cikin kiristocin Duniya suke yi wa al’ummar Musulmi ta hanyar taba janaa’bin Annabi mai tsira da amincin Allah abin takaici ne matuka.

2. Lalle gurbatattu cikin Ahlul kitabi (Yahudu da Nasara) suna yin amfani da kasancewar al’ummar Musulmi suna girmama dukkan Annabawa suna ta takalar su Musulmin ta hanyar taba janaa’bin shugaban dukkan Annnabawa da Manzanni wanda Allah Ya yi masa tsira da aminci shi da iyalansa!

3. Lalle abin takaici ne, kuma rashin mutunci ne a ce mutanen da suke girmama wanda kake ganin shi shugabanka ne amma kuma kai ka rika cin mutincin wanda yake shi shugabansu ne, kuma a hakika ma shugabanka ne.

4. Muna yin tir da Allah wadai da abin da tsageru cikin kiristocin Yarbawa suka rubuta na batanci ga janaa’bin Manzon Allah a cikin jaridarsu.

5. Muna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya kara wa Annabinmu shugaban dukkan Annabawa daraja. Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button