Addini da RayuwaLabarai

An zane wani tsoho dan 63 a bainar Jama’a bisa yiwa surukarsa fyade

An zane wani tsoho dan 63 a bainar Jama’a bisa yunkurin yiwa surukarsa fyade

Daga Manuniya

Wani tsoho dan shekara 63 a Uganda ya sha bulala 10 a bainar jama’a hadi da biyan tarar shs100,000 da kuma akuya guda 1 bisa kamashi yana yunkurin yiwa surukarsa fyade a kauyen Akero dake garin Bukedea.

Manuniya ta ruwaito mutumin mai suna Moses Oluka ya rika kokarin bin matar dansa Alupo Jessica, bayan abun ya ishe ta, sai ta sanar da mijinta Akol Samuel. Nan da nan Dan nasa suka dunguma zuwa wajen shugaban kabilarsu Akol Joseph suka kai masa kara.

Shugaban kabilar bayan yayi bincike sai ya hada taron dattawan garin sannan ya gayyato wanda ake zargin.

A wajen taron kabilar ne aka tattauna zargin inda aka sami tsohon da laifin da ake tuhumarsa kuma anan take aka yanke masa hukuncin bulala 10 a bainar jama’a, sannan ya siyo dan bunsuru guda daya sannan aka ci shi tarar 100,000 kudin Uganda

Majiyar MANUNIYA ta ruwaito lamarin ya faru ne a ranar Talata, 27 ga watan Yuni da muke ciki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button