Daga Manuniya
Mutumin da ake zargi yayi yunkurin soka wa shugaban kasar Mali, Assimi Goita wuka a masallacin idi ya mutu a kurkuku
Gwamnatin kasar Mali ce ta sanar da mutuwar mutumin a ranar Lahadi.
A cewar sanarwar rashin lafiya mai tsanani ta kama mutumin a kurkuku aka kwashe shi zuwa asibitin a cen rai yayi halinsa.
Sai dai Gwamnatin kasar ta ce zatayi binciken musabbabbin mutuwar mutumin wanda aka ki bayyana sunansa.