in ,

KANO: Hadarin mota ya kashe mutum 18 da wasu yan gida daya su 6

Hadarin mota ya kashe mutum 18 da wasu 6 yan gida daya a Kano

Daga Manuniya

Hadarin mota ya kashe akalla mutum 18 da wasu mutum 6 yan daki daya a karamar hukumar Doguwa dake jihar Kano.

Manuniya ta tattara rahoton cewa hadarin ya rutsa da iyalin wani
Malam Bashir Doguwa wanda ya kwashi iyalinsa su 6 daga garin Doguwa zasu je ziyaratar daya diyarsa Firdausi Bashir a makarantar Sakandaren mata ta First Lady Secondary School dake Dambatta wacce take kan rubuta jarabawar NECO

Shugaban hukumar kiyaye hadurra ta kasa reshen jihar Kano Zubairu Mato ya ce hadarin ya faru ne a ranar Juma’a 23 ga watan Yuni da muke ciki a daidai gadar Shiburu inda motar tasu kirar Volkswagen Sharon ta afka rafi sakamakon karyewa da gadar tayi saboda ambaliyar ruwa.

Wani da abun ya faru a gaban idonsa ya shaidawa majiyar Manuniya cewa dreban bai fahimci gadar ta karye ba sai da ya zo gab, wajen kokarin kaucewa sai motarsu ta afka rafi kuma nan take duka fasinjoji 18 dake ciki suka mutu.

Iyalan Malam Bashir 6 dake cikin motar sun hada da shi kansa Malam Bashir Doguwa, da Malami Gidan Tanimu Doguwu, da Safiya Mukhtar Doguwu, da Shashida Bashir me goro Doguwu, da Fatima rabi u me goro Doguwu, da Uzairu Bashir me goro Doguwu, dukansu iyalan margayin kuma yan garin karama hukumar Doguwa ta jihar Kano.

Manuniya ta ruwaito tuni akayi jana’izar duka mamatan washe gari ranar Asabar.

Ana kashe mutane suna karkatar da kudin makamai wajen kasuwancinsu

DA DUMI-DUMI: Majalisa ta bukaci Ganduje ya kori Muhwayi. Zata bincike shi daga 2015-2021