Addini da RayuwaLabarai

El-Rufai ya fara rabon gidaje 452 da ya gina wa masu karamin karfi

El-Rufai ya fara raba gidaje 452 da ya gina domin masu karamin karfi a Kaduna

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna ya sanar da fara bayar da rukunin gidaje 452 da ya gina domin masu karami da matsagaicin karfi a jihar.

Gwamnan ya gina gidaje 228 a yankin Rigasa ta wajen titin zuwa Airport sai kuma gidaje 224 a Ungwan Tanko dake bayan NNPC.

A wata sanarwa da ma’aikatar Gidaje da tsara birane da muhalli ta fitar ta ce farashin gidajen sun fara daga N4,230,000, zuwa N5,170,000 sai kuma daki bibbiyu akwai na N6,570,000 da na N7,372,000 sannan akwai kuma daki Uku akan farashin N9,025,000

Sanarwar ta ce daga Kungiyoyi da yan kasuwa har zuwa daidaikun mutane kowa nada damar mallakarsu matukar mutum mazaunin Jihar Kaduna ne.

Domin Mallakar gidajen ko karin bayani sai a tuntubi ma’aikatar gidaje da birane wato “Ministry of Housing and Urban Development” dake No 3 Sokoto Road, Kaduna ko a kirasu a 0803 590 0918 ko 0802 220 0451

Karin bayani kan yadda za a iya mallakar gidajen

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button