Labarai

DA DUMI-DUMI: Majalisa ta bukaci Ganduje ya kori Muhwayi. Zata bincike shi daga 2015-2021

Majalisa ta bukaci Ganduje ya kori Muhwayi, zata bincike shi daga 2015

Daga Manuniya

Majalisar dokokin Kano ta bukaci Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje ya kori dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da karbar korafi ta jihar Kano, PCAA Muhuyi Magaji daga aiki gaba daya sannan ya kama shi.

Manuniya ta ruwaito a zaman majalisar na yau ta bukaci Gwamnan ya bincikeshi sannan ya mika shi hannun hukuma.

Kazalika a nata bangaren majalisar dokokin ta kafa kwamitin mutum 6 da zasu binciki Mista Muhwayi tun nadashi shugabancin hukumar a 2015 zuwa 2021 da aka dakatar dashi.

Muhuyi Magaji dai shine ya binciki tsohon Sarkin Kano a karkashin hukumar karbar korafin da ya jagoranta inda ya bukaci Gwamnan Kano ya kori Sunusi Lamido Sunusi II daga Sarkin Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button