Labarai

Buhari zai tafi jinya London sai tsakiyar August zai dawo

Daga Manuniya

Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi zuwa London a yau Litinin 26 ga watan Yuni domin halartar wani taro na duniya kan shirin tara kudi don inganta ilimi a kasashen duniya tsakanin shekarar 2021 zuwa 2025.

Manuniya ta ruwaito daga nan kuma zai tsaya na wasu yan kwanaki a kasar domin duba lafiyarsa.

Taron wanda Firaiministan Burtaniya Boris Johnson zai karbi bakunci da kuma shugaban Kenya Uhuru Kenyatta zai samu halartar shugabannin kasashen da masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi da shugabannin matasa domin hada kai wajen samun mafita kan harkokin ilimi.

A sanarwar da kakakin Shugaban kasa Femi Adesina ya fitar ya ce Buhari zai kuma yi wata tattaunawa ta musamman da Firaiministan Burtaniya Boris Johnson.

Ya ce ana sa rai shugaban kasar zai dawo Nigeria mako biyun farkon watan Augusta 2021.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button