Labarai

Ana kashe mutane suna karkatar da kudin makamai wajen kasuwancinsu

Daga Manuniya

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, yace abun takaici ne ace hatta jamhuriyar Nijar ta fi Nigeria tsaro duk da makudan kudaden da ake kashewa a fannin tsaro a Nigeria ya ninka wanda Nijar ke kashewa tsaron ta.

Majiyar Manuniya ta ruwaito Sani a tattaunawarsa da AIT yace kusan ana iya cewa jami’an tsaro sun koma karkatar da kudaden da ake ware masu na makamai wajen gina kasuwancinsu, A cewarsa ko a kwanan nan sai da Ministar kudi, Hajia Zainab Ahmed tace ta baiwa fannin tsaro N1.3 trillion a cikin watanni 28 baya ga kudade na musamman da suke karba daga wajen shugaban kasa ta karkashin kasa.

Amma abun kunya a cewar Sanatan duk da wadannan kudade da ake kashewa fannin tsaro yan ta’adda masu rike bindigar AK47 sai cin karensu babu babbaka suke yi a kasar nan. Saboda kafin yanzu manyan jami’an tsaro sun karkatar da kudaden suna gina jami’o’i da shaguna da otel-otel.

A cewar Sanatan tabarbarewar tsaro a kasarnan yayi munin da ya kamata ace Gwamnati ta jingine batun gina ayyukan more rayuwa ta dukufa wajen lalubo mafita kan tsaron da ya addabi jama’a.

“Jihar Kaduna ta fi kowace jiha tabarbarewar tsaro domin a yanzu masu garkuwa da mutane sun mamaye duka kananan hukumomi 21 daga cikin 23 dake jihar idan ka cire birnin Kaduna babu inda akwai tsaro” inji Sani.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button