in ,

Ya fita sayen abinci ya rotsa motar N30m daga bashi wanki

Daga Manuniya

Tsautsayi ko ganganci? Wani mai wankin motoci ya gamu da ta kansa bayan da ya dauki motar wani Alhaji bayan ya kai masa wanki ya tafi da ita sayo abinci kwatsam ya gamu da hadari inda nan take yayi kwatsa-kwatsa da motar.

Kodayake dai shi bai ji ko kwarzane ba amma dai gaban dalleliyar motar tayi rugu-rugu fiye da tunani.

A wani bincike da Manuniya tayi na farashin motar wata fara kirar Mercedes Benz GLC farashin ta a beljon ta kai kusa miliyan 25 zuwa 30 a Nigeria.

A wani bidiyo da ya karade kafafen sadarwa an ga mai wankin motar yayi kwance a kasa shabe-shabe yana baiwa Alhaji mai motar hakuri yana neman afuwa.

Shin wannan tsautsayi za a kirashi ko ganganci?

Shisha tafi sigari illa, tana jawo kansa da hana haihuwa –inji masana

Mutumin da ya kaiwa shugaban Mali hari da wuka ya mutu a kurkuku