Labarai

Dalibai 156: Masu garkuwa sun karbe N55m sun rike wanda ya kai kudin sai an basu kari

Dalibai 156: Masu garkuwa sun karbe N55m sun rike wanda ya kai kudin sai an basu kari

Daga Manuniya

Iyayen daliban Islamiyyar Salihu Tanko su156 da akayi garkuwa dasu a Tegina, dake karamar hukumar Rafi a jihar Niger sun koka kan cewa barayin yaran sun ki sako daliban duk da an basu kudin fansa har Naira Miliyan 55.

Shugaban makarantar Malam Alhassan Garba Abubakar, ya shaidawa majiyarmu cewa da farko sun tura Naira miliyan 25 amma bayan kwanaki 3 sai masu garkuwar suka ce anyi kuskure ba su aka baiwa kudin ba, wasu gungun aka baiwa saboda haka sai a sake turo masu Milyan 30.

Alhassan ya ce bayan iyayen yaran sun dage sun sake yin karo-karo sun hada miliyan 30 suka tura wani Kassim Tegina amma sai yan bindigar suka rike shi saboda wai sun kirga kudin bai cika ba.

Manuniya ta ruwaito a karo na biyu yan bindigar sun ce sai iyayen yaran sun cikaso Naira miliyan N4.6million. Kana kuma sai sun sayo masu babura kirar “Honda” guda 6

Kowane babur da suka nema akalla ana sayar da duk guda daya Naira N490,000 kenan suna bukatar karin Naira N6million.

Sai dai Iyayen daliban sun ce a yanzu babu ko sisi da zasu iya karawa domin sunyi iya kokarinsu don haka sun barwa Allah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button