in

“Yanzu nine uban ku” -El-Rufai ya fadawa iyalan margayi Bantex cikin kukaDaga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya sharbi kuka a lokacinda yake jawabin bankwana ga iyalan tsohon mataimakinsa Barnabas Bala Bantex a gidan Gwamnatin jihar Kaduna

El-Rufai yayi jawabai masu ratsa zuciyata na yabo da bayyana wasu kyawawan halaye na tsohon mataimakin Gwamnan wanda ya rasu makon da ya gabata kuma ake shirin bizne shi.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan wanda kuka ya kwace masa yana tsakiyar jawabi ya bukaci iyalan tsohon mataimakin nasa su zo gareshi ga duk wata damuwa ko bukata tasu “Banex amini ne gareni tun a makaranta har zuwa kasuwanci da sha’anin Gwamnati, lallai nayi rashin babban aboki kuma amini nagari, don haka yanzu na zama uba gareku (iyalan Bantex) ku zo gareni kan duk wata bukata taku” nan kuka ya kwacewa Gwamnan

An gano mutumin da ya bace shekara 47 daga aikensa shago sayo shinkafa

Kotu ta janye cigaba da sauraron karar hana tsige mataimakin Gwamnan Zamfara