Labarai

Rashin kai hari ko tashin bom a sallar bana alama ce ta’addanci ya zo karshe a Nigeria –inji Buhari

Rashin tashin bom ko daya a sallar bana alama ce ta’addanci ya zo karshe a Nigeria –Buhari

Daga Manuniya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ikirarin cewa a sallar idin bana 2021 ba a samu rahoton kashe rai ko tashin bom ko daya a fadin Nigeria ba kuma hakan tamkar alama ce dake nuna hare-haren ta’addanci ya zo karshe a kasar

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina, a wani jawabi da ya fitar mai taken “Allah yayi wa sojojinmu albarka” ya roki yan Nigeria su rika sanya sojojin kasarnan a cikin addu’oin su.

A cewarsa da yardar Ubangiji nan gaba kadan kashe-kashen rayuka, ta’addanci, satar mutane a karbi kudin fansa da duk wasu tashe-tashen hankula zasu zama tarihi a Nigeria zaman lafiya zai dawo cikin kasar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button