Labarai

Kotu ta janye cigaba da sauraron karar hana tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

Kotu ta janye cigaba da sauraron karar hana tsige mataimakin Gwamnan Zamfara

Daga Manuniya

Alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja Justice Obiora Egwatu a yau Juma’a ya janye kansa daga cigaba da sauraron karar da jam’iyyar PDP ta shigar gabansa tana neman ya dakatar da majalisar dokokin jiharsa Zamfara daga tsige mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Mahadi Aliyu Mohammed Gusau.

Dama dai a makon jiya ne Alkalin kotun ya yanke hukunci majalisar Zamafara da Babban Alkalin jihar Zamfara kada su sake su soma shirin tsige mataimakin Gwamnan har sai an kammala shara’ar da aka shigar gabansa.

To sai dai Manuniya ta ruwaito a yau Juma’a Alkali Egwato ya ce ba zai cigaba da sauraron karar ba saboda ya samu bayanin cewa an shigar da makamanciyar karar a wata kotu  a Abuja

Ya ce cigaba da sauraron karar zai iya kawo rudani da waccen kotun don haka a ya barwa wancen kotun wacce Alkali Justice Inyang Eden Ekwo ke jagoranta ya cigaba da sauraron shara’ar,

Jam’iyyar PDP ce dai ta shigar da karar saboda ta fahimci APC na shirin tsige mataimakin Gwamnan saboda yaki sauya sheka zuwa APC daga PDP kamar yadda Gwamnan jihar Matawalle yayi a watan da ya gabata.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button