Addini da RayuwaLabarai

An gano mutumin da ya bace shekara 47 daga aikensa shago sayo shinkafa

An gano wani mutum da ya bace tun 1974 daga aikensa shago sayo shinkafa

Daga Manuniya

Wani mutum a Kenya mai suna James Mwaura dake zaune a garin Molo, a yankin Nakuru ya hadu da iyalansa bayan shafe shekara 47 da bacewa.

Manuniya ta ruwaito an aiki Mwaura tun a 1974 lokacin yana da shekara 23 shago ya sayo shinkafa amma daga nan ba a sake jin duriyarsa ba har anyi cigiya an gaji.

Mista Mwaura, wanda a yanzu yake da shekara 70 yace yayi makuwa ne a lokacin sai dai kwatsam ya tsinci kansa a Nairobi, shikuma daga nan ya wuce garin Naro Moru dake yankin Nyeri ya cigaba da rayuwasa har yayi aure ya haifi yara 3 da jikoki 4.

Mwaura sanye da “bluen taguwa” ya gamu da wani danginsa ne a shafin Facebook wanda suka tattauna har Allah yasa suka gane juna aka kawoshi gida cikin iyalansa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button