Labarai

Sheikh Abduljabbar ba lafiya yana kashin jini a kurkuku –inji Lauyansa

Sheikh Abduljabbar ba lafiya yana kashin jini a kurkuku –inji Lauyansa

Daga Manuniya

Rahotanni daga jihar Kano na bayyana cewa rashin lafiya ya kama mutumin nan mai ikirarin malumta, Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara a kurkukun da ake tsare dashi har ta kai yana kashin jini.

Sai dai bayanai a baya-bayan nan sun ce babu abun daga hankali akai.

A wani bincike Manuniya ta ruwaito tuni lauyansa ya je da likita yayi masa yan tambayoyi tare da gwaje-gwaje ya rubuta masa magunguna sannan ya bada shawarwari akan abubuwan da ya kamata a yi kafin sakamakon gwaje-gwajen da akayi masa su fito.

Abduljabbar dai yana fuskantar hukunci ne daga mahukuntan Kano sakamakon kalamai mararsa kan gado da yayi akan addinin musulunci kuma da aka mukabalance shi akai ya kasa kare kansa da hujjoji.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button