Labarai

Sarkin Muri ya bawa yan fashin daji kwana 30 su fice daga Taraba

Daga Manuniya

Mai Martaba Sarkin Muri, Alhaji Abbas Njida Tafida, ya baiwa yan fashin daji kwana 30 su fice daga dazuzzukan jihar Taraba ko kuma yasa a fito dasu da karfin tsiya su fuskanci mummunan hukunci.

Ya ce zai bawa jama’a umurni suyi fito na fito dasu.

Sarkin wanda ke jawabi jim kadan bayan idar da sallar idi Manuniya ta ruwaito yana cewa umurnin ya zama wajibi ne duba da yadda duk wani tashe-tashen hankula, kashe-kashe da sace-sacen jama’a ana karbar kudin fansa, da fyade ake danganta shi da Fulani.

Manuniya ta ruwaito Alhaji Abbas ya umurci shuwagabannin Fulani a jihar Taraba su gaggauta kwakulo miyagun cikinsu dake wannan danyen aiki.

Sarkin ya kara da gargadin hukumomi dake bayar da belin yan bindigar idan an kama an kai masu da su kuka da yin hakan domin daga yanzu zai sa a rika kashe duk dan bindigar da aka kama. A cewarsa da zaran wa’adin kwana 30 din ya cika zai jagoranci jama’a su afka dazuzzukan jihar tare da kashe duk mahalukin da suka samu a ciki.

“Mun gaji da rashin bacci saboda rashin tsaro, haba mana, abar mutane su ji da bakar yunwa da talaucin da aka jefa su ciki mana” inji Basaraken

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button