in ,

HOTUNA: Ambaliyar ruwa na kassara Yobe Gwamna ya tafi hidimar jam’iyya

A yayinda Gwamna Mai Mala na jihar Yobe ke shan yabo sakamakon fadi tashin da yake yi domin daidaita sahun jam’iyyar APC wasu na ganin tamkar Gwamnan ya saki farilla ne ya kama mustahabbi domin ya bar jiharsa cikin wani hali.

Rahotannin da Manuniya ta tattaro ya nuna ko a wannan makon al’ummar karamar Hukumar Jakusko sun shiga halin kunci da damuwa sakamakon yadda ambaliyar ruwan sama ya rusa gidaje da dumbindukiyoyi.

Bayanai sun nuna jama’ar garin sun bazama neman doki wanda bayan jerin koke-koke an hangi Hukumar bada agajin gaggawa ta rarrafa ta leka kauyakun da abun ya shafa. Sai dai babu wani kwakkwaran agaji da aka ga ya fita daga Gwamnatin jihar ko Hukumar ta SEMA.

Wannan dai kadan ne daga dumbin matsaloli da halin kuncin da jama’a ke fuskanta a Yobe saboda rashin zaman Gwamnan

Sarkin Muri ya bawa yan fashin daji kwana 30 su fice daga Taraba

An gano mutumin da ya bace shekara 47 daga aikensa shago sayo shinkafa