Labarai

2023: APC tayi kafuwar da babu mai iya jijjiga ta -inji fadar shugaban kasa

PDP ta daina mafarkin cin zabe a 2023 APC tayi kafuwar da babu mai iya jijjiga ta -inji fadar shugaban kasa

Daga Manuniya

Fadar shugaban kasa ta gayawa jam’iyyar adawa ta PDP cewa ta farka daga baccin da take yi na tunanin zata iya cin zabe a 2023 domin har gobe talakawa suna tare da Buhari kuma duk inda ya karkata cen zasu bi a babban zaben 2023.

Da yake magana jim kadan bayan sallar idi a Daura mai magana da yawun shugaban kasa Mallam Garba Shehu, ya ce irin soyayya da goyon bayan da talakawan Nigeria ke yiwa Buhari so na har abada ba zasu juya masa baya ba, balle kuma a yanzu da yan Nigeria suka sha romon Dimokuradiyya a mulkinsa.

Manuniya ta ruwaito Garba Shehu na fadin cewa APC tayi kafuwar da wata jami’iyya ba zata iya jijjigata ba. Dadin dadawa kuma ga dumbin ayyukan da take shararawa yan Nigeria, sannan ga romon Dimokuradiyya da talakawa ke sharba tun hawan Gwamnatin Buhari a karkashin APC

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button