Labarai

Wani lauya ya shigar da kara a cire Nigeria daga kasashen musulunci

Wani lauya ya shigar da kara a cire Nigeria daga kasashen musulunci

Daga Manuniya

Lawyer sues FG over Nigeria’s membership of OIC

Wani lauya mai raajin kare yancin dan Adam ya shigar da Gwamnatin tarayya kara yana neman kotu ta haramta wa Nigeria cigaba da kasancewa mamba a kungiya kasashe musulmai ta duniya wato OIC (Organisation of Islamic Countries).

Lauyan mai suna, Malcom Omirhobo ya nemi babbar kotun tarayya dake Abuja ta kuma haramta wa duka jihohi 36 na Nigeria da Abuja daga alakanta kansu da wani addini ko nuna fifiko kan wani addini ko bin tsarin wani addini a hukumance a jihohinsu.

Manuniya ta ruwaito lauyan na cewa Nigeria kasa ce ta kowa da kowa wacce ke dauke da mutane fiye da miliyan 200 dake bin addinai da al’adu daban-daban don haka zamewar Nigeria a matsayin mamba a kungiyar kasashen musulmi ya saba dokar kasa sannan tamkar nuna wa duniya ne cewa Nigeria kasar musulmi ce.

Don haka lauyan ya nemi kotu ta haramta wa Nigeria cigaba da kasancewa a OIC, ko bayar da wani tallafi ko gudunmuwa daga baitul malin kasar zuwa kungiyar ta OIC.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button