Labarai

Matasa sun ki karbar tallafin shinkafa daga dan majalisa, su aiki suke bukata

Matasa sun ki karbar tallafin shinkafa daga dan majalisa, su aiki suke bukata

Daga Manuniya

Wasu gungun matasa a Ghana sun mayar wa wani dan majalisa mai wakiltar Damongo buhunan shinkafar da ya tura a rarraba masu domin yin bukukuwan Sallar layya a mazabar tasa.

Manuniya ta tattara rahoton matasan sun nemi dan majalisar idan dagaske yake yi to ya nema masu ayyukan yi da zasu dogara da kansu a madadin kashe masu zunciya da yake yi yana mayar dasu cima zaune da tallafin kayayyakin abinci.

A wani bidiyo da Manuniya ta kalla anga yadda matasan mazabar ta Damongo wacce dan majalisa, Hon. Samuel Abu Jinapor ke wakilta ke ihun bama so tare da jefa buhunan shinkafar da ya aike masu cikin motar da ya turo aka kawo abincin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button