Labarai

Jami’an tsaro sun kama Sunday Igboho a Cotonou yana hanyar tserewa Germany

Jami’am tsaro sun samu nasarar kama shugaban yan aware mai fafutikar kafa kasar Yarabawa ta Oduduwa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho

Manuniya ta ruwaito yan sandan jamhuriyar Benin ne suka kama shi a Cotonou yana shirin tserewa zuwa kasar Germany a daren jiya Litinin.

Sunday Igboho dai ya sha bugun kirjin cewa yafi karfin hukumomin Nigeria a lokacin da suka bayyana suna nemansa ruwa a jallo. Dan awaren ya sha alwashin raba Nigeria da sauran surutai da cika baki da yayi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button