Addini da RayuwaLabarai

El-Rufai ya lashe Kambun Gwarzon Gwamnan Shekara a Lagos

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya lashe kambun Gwarzon Gwamnan Shekara na jaridar Vanguard wato “THE VANGUARD GOVERNOR OF THE YEAR”

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya yi wa takwarorinsa zarra ne a bikin karramawar wacce ta gudana a a daren yau Asabar a Eko Hotels dake jihar Lagos.

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya samu rakiyar mai dakinsa Aisha Ummi Garba El-Rufai

El-Rufai dai yayi kaurin suna wajen rufe ido yana yin wasu aikace-aikacen da kirkiro wasu kudurori da suka fara farfado da kima da martabar jihar Kaduna kodayake dai yana fuskantar suka da korafe-korafe daga sassan jihar sannan masu hasashen siyasa na ganin abunda yake yi ya dace amma kuma kasadace babba da zata iya jawo masa disashewar farin jininsa a siyasance.

Sai dai Gwamnan ya sha wanke kansa da Gwamnatinsa game da wasu zafafan kudurori da yake dauka kuma yakan ce ‘baya shakkar abunda hakan ka iya jawo masa a siyasance domin shi burin shi dawo da kimar jihar Kaduna kuma anan gaba za aga amfanin tsauraran matakan da ya dauka’

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button