Labarai

N2Bn: Maina ya kasa bayyana a kotu saboda guiwoyinsa na ciwon

Badakalar N2Bn: Maina ya kasa bayyana a gaban kotu saboda guiwoyinsa na ciwon

Daga Manuniya

Jami’an gidan yarin Kuje sun kasa gabatar da tsohon shugaban hukumar kula da yan fansho ta kasa Abdulrasheed Maina a kotu saboda yana fama da ciwon guiwa.

EFCC ce dai ta gurfanar da Maina bisa zargin yaci kudin yan fansho har Naira Biliyan biyu da miliyan dari (N2.1Bn).

Sai dai Manuniya ta ruwaito a zaman kotun na yau, wani jami’in kula da yan gidan yarin kuje ya gayawa alkalin babban kotun Abuja, Justice Okon Abangkotu cewa sun zo da wanda ake zargin wato Abdulrasheed Maina amma ba zasu iya shigo dashi cikin kotu ba sun ajiye shi a waje cikin mota saboda duka guiwoyinsa suna yi masa ciwo.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button