Labarai

Ingila zata hukunta Nigeria da Kenya bisa kama Nnamdi Kanu ba izini

Daga Manuniya

Ingila bata gamsu da hanyoyin da aka bi wajen kwamuso Nnamdi Kanu daga Kenya zuwa Nigeria ba kuma zata kalubalanci yin hakan sannan zata hukunta duk jami’in Nigeria ko Kenya da ta samu da hannu a ciki.

Lauyan Nnamdi Kanu na Nigeria Aloy Ejimakor ne ya bayyana haka a ranar Alhamis jim kadan bayan ya kammala wata ganawa da shugaban na IPOB a kurkukun da ake tsare dashi.

Ejimakor yace ya kaiwa Nnamdi Kanu wasu takardu guda Biyu daya daga ofishin jakadancin Birtaniya daya kuma daga kamfanin Lauyoyinsa na Ingila, wato Bindmans, domin ya sanya hannu amincewa hukumomin su shiga cikin shari’ar tasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button