WATA SABUWA: Ganduje yaci Ja’afar Ja’afar tarar Naira Biliyan Uku a Kotu
Daga Manuniya
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya sake shigar da mawallafin jaridar DAILY NIGERIAN, Jaafar Jaafar da kamfaninsa na Penlight kara a gaban wata babbar kotu dake Abuja bisa zargin bata masa suna.
Manuniya ta ruwaito Ganduje ya nemi Ja’afar Ja’afar da kamfaninsa su biyashi tarar akalla Naira Biliyan 3 (N300B) a bisa wani bidiyo da Daily Nigerian ta wallafa tana ikirarin cewa Gwamnan ne ke sankame Dala a babbar rigarsa
A sabuwar karar dai Gwamnan ya nemi kotu ta cigaba da sauraron kara har ta yanke hukunci ko da Ja’afar Ja’afar din bai bayyana a gabanta ba. Manuniya ta ruwaito yanzu haka dan jaridar na gudun hijira a London