Labarai

An kwaso Jiragen yakin da Buhari ya sayo a kasar Amurka zuwa Nigeria

Daga Manuniya

Rundunar sojin sama ta Nigeria ta nuna hotunan rukunin farko na wasu jiragen yaki guda 6 kirar A-29 Super Tucano da ta sayo a Amurka kuma ake kan hanyar kawo su Nigeria

Kakakin rundunar sojin sama Edward Gabkwet ya shaidawa Manuniya cewa jiragen sun taso tun ranar Laraba, 14 ga watan Yuni 2021 kuma ana sa ran zasu iso Nigeria nan da karshen watan Yuni da muke ciki.

Ya ce jiragen yakin zasu bi ta kasashe 5 kafin su iso Nigeria. Kasashen sune Canada, da Greenland, da Iceland, da Spain da kuma Algeria

Kalli hotunan a kasa

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button