Labarai

Wata bazawara a Kano ta ce idan ba Ganduje ba sai rijiya

Rahotanni sun karade kafafen sadarwa na wata zanka-dediyar Bazawara mai suna Nana Adam Janbulo, wadda ake fi sani da mai Muryar Madara ta ce a gaskiya a rayuwarta tana masifar son Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Kuma so na hakika na Aure

A cewarta, zuciyarta ta dade ta na son shi, amma ta rasa ta ya ya za ta fada masa. Gashi soyayyarsa na ta ci mata jiki ta rasa yadda zata yi, “kuma auren shi na ke son yi” a cewar wasu kafafen yada labarai da suka ruwaito labarin

Sai dai Nana ta nemi makusantan gwamna Ganduje da su taimaka su hada ta da shi domin ganin wannan mafarki nata ya zama gaskiya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button