Labarai

An kama wani tsoho dan shekara 60 dake yiwa masu garkuwa da mutane dakon bindigogi

An kama tsoho dan shekara 60 dake yiwa masu satar mutane dakon bindiga

Daga Manuniya

Rundunar yan sanda ta musamman karkashin Abba Kyari sun kama wani tsoho dan shekara 60 mai suna Umaru Mohammed dake yiwa masu garkuwa da mutane a manyan tituna dakon makamai daga Arewa zuwa yankin Kudu maso Yamma a motarsa.

Manuniya ta ruwaito tsohon ya ce yan bindigar suna biyansa Naira Dubu Dari Biyu idan ya kai masu makaman a wajen da suke shirin kai hari a babban hanya sannan suna kara mashi wata dubu 200 bayan sun karbi kudin fansa idan yaje karban makaman zai kai masu waje na gaba.

Tsohon ya ce yana samun sa’a kan jami’an tsaron hanya basa binciken motarsa don  suna masa kallon shi tsoho ne ba zai yi ta’addanci ba.

Manuniya ta ruwaito an kama tsohon da yan gungunsa sannan an kwato makamai da albarusai da dama daga hannunsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button