Labarai

Dubban mutane sun shigar da karar kada abar Biloniya Jeff ya dawo Duniya bayan ya tafi shawagi duniyar wata

Dubban jama’a sun shigar da karar a hana  shugaban Amazon, Biloniya Jeff Bezos izinin dawowa duniya bayan ya tafi duniyar wata yin shawagi

Daga Manuniya

Manuniya ta ruwaito daga majiya mai tushe cewa kawo yanzu fiye da mutum dubu goma sha Biyu (12,000) ne suka shigar da kara a kasar Amurka suna neman kada Gwamnatin kasar ta baiwa shugaban kamfanin shagon sayar da kaya na Amzon kana mashahurin mai kudi Biloniya, Jeff Bezos izinin dawowa cikin duniya bayan ya shiga duniyar Wata.

Manuniya ta ruwaito cikin raha aka kirkiri karar amma kan kace kwabo abu ya rikide inda jama’a suka rika tururuwa suna sanya hannu kan karar wacce ke zargin Biloniyan Mista Jeff da burin mallake duniya. Sannan sun ce dama mu’amalolinsa basu yi kama da dan Adam ba.

Dama dai a watan Yuni ne dai Mista Jeff din ya sanar cewa zai je shawagi duniyar wata shi da kaninsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button