Labarai

Gwamnan Niger ya kafa rundunar tsaro ta musamman a Minna

LABARI: Gwamnan Niger ya kafa rundunar tsaro ta musamman da zata yaki ta’addanci a Minna

Daga Manuniya

Gwamna Abubakar Sani Bello ya kaddamar da jami’an tsaron sa-kai na musamman a jihar Niger “Niger Special Vigilante Corps (NSVC)” da nufin su taimaka wajen dakile sara suka da sauran ayyukan laifi da batagarin matasa ke yi a Minna babban birnin jihar.

Sakatariyar yada labarai ta Gwamnan Niger Mary Noel-Berje ta shaidawa Manuniya cewa Gwamnatin Niger ce da hadin guiwar rundunar yan sanda suka kirkiro yan bangar daga manyan kungiyoyin sa-kai na matasa guda 9 dake kwaryar jihar.

Kungiyoyin sun hada da; Chinaka, da ADC, da Abidoka, da WAI BRIGADE, da Hunters Group, da AOG, da Vigilantes, da kuma Maito Maitumbi Security Organisation.

Manuniya ta ruwaito Gwamnan ya basu kyautar motoci kirar Hilux guda 10 da babura guda 20 da sauran kayan aiki.

“Wannan shine rukuni na farko na shirin ana sa ran za a yi rukuni na 2 anan gaba domin ganin an samu tsaro a fadin jihar Niger. Ayyukan NSVC a yanzu zai takaitu ne a iya birnin Minna anaso a yayinda yan sanda da sauran hukumomin tsaro ke yaki da masu garkuwa da mutane da yan bindiga a sauran sassan jihar sai su kuma NSVC su bayar da tsaro a kwaryar birnin jihar” inji Mary Noel-Berje

Shima a nasa jawabin Kwamishinan yan sandan Niger CP Adamu Usman ya jinjinawa Gwamna Abubakar Sani Bello bisa kwarin guiwa da hadin kai da yake baiwa jami’an tsaro a kokarinsu na kawo karshen ta’addancin yan bindiga a jihar.

Ya ce a wannan karon sun baiwa matasa 161 na NSVC horo na musamman domin su bayar da gudunmuwar da ake so a fannin tsaron jihar. Manuniya ta ruwaito taron ya gudana ne a hedkiwatar rundunar yan sanda ta jihar Niger.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button