Labarai

KADUNA: Yan sanda sun dakile harin yan bindiga a Tudun Wada

Yan sanda sun fatattaki yan bindiga a Tudun Wada Kaduna

Daga Manuniya

Rundunar yan sandan jihar Kaduna ta samu nasarar dakile yunkurin wasu yan bindiga na aiwatar da hari a Jada Road dake Tudun Wada Kaduna.

Wani mazaunin yankin mai suna Kabir Sani ya shaidawa Manuniya cewa jama’ar unguwar ne suka lura da wasu mutane 3 a cikin mota suna ta kai-komo lamarin da yasa suka yi saurin sanar da ofishin yan sanda.

Manuniya ta ruwaito da zuwan yan sanda sai mutanen suka fara bude wuta amma cikin ikon Allah yan sandan sun fatattake su har ma suka samu nasarar kwace motar da suke ciki wata Toyota Corolla LE.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Kaduna, Muhammad Jalinge ya tabbatar da faruwar lamarin. Ya ce wadanda suka gudu cikin yan bindigar sun gudu da raunuka kuma yana rokon jama’ar gari su sa ido da zaran sun ga mai jinyar raunin da basu gamsu dashi ba su gaggauta sanar da hukumar yan sanda

Ya ce yan bindigar sun shiga wata Toyota Corolla LE, mai ruwan toka da lambar Abuja wato ABJ 704 MX.

Yace sun samu takardar lasisin tuki ta “Driving license” da wasu katinun banki wato “ATM cards”.

Kazalika yace sun samu albarusai da sauran makamai a cikin motar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button