Labarai

KALLI HOTUNA: Wani barawo ya mutu a cikin silin din gidan da yaje sata

INDA RANKA: Wani barawo ya mutu a cikin silin din gidan da yaje yin sata

Daga Manuniya

Wani abun tashin hankali ya faru a Unguwar Rimin jihar Kaduna a ranar Lahadi da ta gabata bayan da sanyin safiyar ranar Lahadi aka fara jin wani irin wari da doyi a wasu shaguna a Unguwar Rimi kusa da gidan man Total,

Manuniya ta ruwaito ko da aka bincika sai aka ga ashe wani da ake zargin Barawo ne yashiga cikin silin da nufin ya haura ciki yayi sata sai kuma kusa ta chake shi a ciki ya fadi ya mutu kusan kwana Uku babu wanda yasani har sai da ya fara wari da doyi kafin aka ankara aka shiga aka ciroshi a mace.

Wani ganau a lamarin Najib Bawa ya shaidawa Manuniya cewa an rasa gane ko waye barawon saboda ya kumbura kamanninsa sun sauya gaba daya.

Manuniya ta ruwaito nan da nan aka sanar da ‘yan sanda inda suka tafi da gawar

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button