Labarai

Yajin Aiki Na Biyu: Ba zamu sake yarda NLC ta Katse wuta ba don Bom din mu na iya fashewa

Rundunar Sojoji ta ce ba zata sake yarda NLC ta katse wutar lantarki a Kaduna ba don gudun fashewar Bama-bamai da aka adana

Daga Manuniya

Rundunar Sojojin Nigeria ta gargadi kungiyar kwadago ta NLC daga yunkurin sake katse wutar lantarki a jihar Kaduna a yajin aikin da suke cewa zasu yi karo na biyu.

Rundunar ta ce akwai manyan makamai masu fashewa ciki har da Bama-bamai da ta ajiye a wurare daban-daban a jihar Kaduna wanda zasu iya fashewa, Bama-Baman zasu iya tashi muddin aka dauke wuta na tsawon lokaci. Hukumar sojin ta ce ko a wancen karon da NLC tayi yajin aiki na sojojin sun gargade su tare da nuna masu hadarin dauke wuta ga hukumar sojin amma kungiyar kwadago tayi kunnen shegu da gargadin tare da barazanar cewa idan aka maido wuta a Kaduna zasu katse duka wutar Nigeria.

Manuniya ta ruwaito daga Majiyoyi cewa  wancen karon wasu dalilai ne kawai suka hana sojojin daukar mataki amma wannan karon ba zasu zura ido a sake maimaitawa ba.

Sojojin sun kawo misalai da abunda ya faru a Ikeja Cantonment dake jihar Lagos a ranar 27 ga watan January, 2002, inda Bama-bamai suka fashe sakamakon tangardar wutar lantarki har yayi sanadiyyar turmutstsun da ya jawo mutuwar akalla mutum 1,000

Fashewar Bama-baman ya girgiza jihar Lagos inda gidaje da suke da nisan tazarar Mile 30 sai da suka rushe hakan ya jawo akalla mutum 12,000 suka rasa muhallinsu suka zama yan gudun hijira.

Rundunar Sojojin ta ce tana bakin kokarinta wajen hada injin janareto masu karfi amma duk da haka akwai bukatar wutar domin a samu kwanciyar hankali kan Bama-baman da aka adana “saboda akwai hadari idan aka samu matsalar wuta

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button