DA DUMI-DUMI: Hedkiwatar tsaro ta sanya sojoji cikin shirin ko ta kwana domin dakile zanga-zangar kifar da Gwamnatin Buhari
Daga Manuniya
Rahotanni na bayyana cewa hedkiwatar tsaron Nigeria ta sanya sojoji cikin shirin ko ta kwana a wani gagarumin shiri na tsaro domin tabbatar da masu zanga-zangar “June 12 Protest” domin nuna kin jinin Gwamnatin Buhari basu samu nasara ba.
Dama dai gamayyar yan sa kai da sukayi zanga-zangar EndSars na shirin yin wata zanga-zanga da suka ce sai ta kifar da Gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Dimokuradiyya wato 12 ga watan Yuni da muke ciki.
Sai dai majiyoyi sun ce an sanya tsauraran matakai tare da baiwa sojoji oda su dakile duk wata barazanar tsaro