Labarai

DA DUMI-DUMI: Gwamnan Bauchi ya sauke SSG, Chief of Staff da duka Kwamishinoninsa

Daga Manuniya

Gwamnan jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad ya sauke duka Kwamishinoninsa, da masu bashi shawara da sakataren Gwamnatin jihar, SSG da Shugaban ma’aikatan fadar Gwamnati.

Manuniya ta ruwaito saukewar bai shafi mai bashi shawara kan fannin tsaro ba da mai bashi shawara kan harkokinsu majalisa da kuma mai bashi shawara kan harkokin yada labarai.

Sanarwar ta ce saukewar ya fara aiki nan take. Gwamnan ya godewa duka mukarraban nasa kana ya bukaci su mika ragamar aiki ga manyan sakatarorin ofisoshinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button